News
Da Ɗumi-ɗumi: Tsohon Gwamnan Kwara Ya Faɗa Komar Hukumar EFCC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon Gwamnan Jihar Kwara State, Abdulfatah Ahmed, ya faɗa a komar Hukumar EFCC bisa zargin almundahana biliyoyin Naira a lokacin mulkinsa.
News Point Nigeria ta rawaito cewa, an ga lokacin da Ahmed ya isa ofishin EFCC na Ilorin da safiyar ranar Litinin.
Majiyar ta tamu ta ƙara da cewa EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan ne don amsa mata tambayoyi dangane da yadda ya kashe kuɗaɗen da ake ya wawushe a lokacin mulkinsa a jihar.
Ahmed ya yi gwamnan Kwara ne daga 2011 zuwa 2019 inda ya miƙa mulkin jihar ga Abdulrahman Abdulrazaq.
Ko a shekarar 2021 EFCC ta gayyaci Ahmed ɗin zuwa babban ofishinta da ke Jabi a Abuja bisa zargin alaƙarsa da badaƙalar karkatar da Naira biliyan 9 daga asusun Hwnatin Kwara.
Advertisements
