Connect with us

News

An Sake Babban Rashi A Rundunar Sojin Nijeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Aƙalla sojojin Nijeriya shida sun riga mu gidan gaskiya sakamakon kwanton-ɓaunan da mayaƙan Boko Haram suka yi musu a hanyar Biu-Buni Yadi a Jihar Borno.

Advertisement

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya auku ne a ƙauyen Kamuya da ke kusa da Buratai, mahaifar tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Lt. Gen Tukur Buratai (mai murabus).

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tsinci Gawar Wata Budurwa Mai Shekaru 14, A Ban Dakin Wani Otel 

Majiya ta kusa da rundunar tsaro ta ce, jami’an sun cimma ajali ne a kan hanyarsi ta zuwa Damaturu don shan mai.

Advertisement

“Abin baƙin ciki ne ainun, sojojin runduna ta 135 Special Force BN FOB ne da ke Buratai. An yi musu kwanton-ɓauna ne a hanyarsu ta zuwa shan mai a Damaturu, Jihar Yobe.

“Mun rasa babban janmi’ guda da direba da maharbi da wasu ‘yan rakiya huɗu, yayin da an kwashi waɗanda suka jikkata zuwa aisibiti inda ake yi musu magani,” in ji majiyar.

Advertisement

Wannan na zuwa ne mako guda da yin jana’izar wasu sojoji da masu tada ƙayar baya suka kashe a Jihar Delta a babbar maƙabarta dake Abuja.

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending