News
Rayuwar ‘yan Najeriya da dama ta tabarbare matuka sakamakon tashin farashin kayan masarufi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rayuwar ‘yan Najeriya da dama ta tabarbare matuka sakamakon tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ya tilasta fita wajen neman abinci da kuma cin shinkafa mara kyau, wadda a da ake amfani da su wajen ciyar da kifi, wasu rahotanni na nuni da cewa cewa wasu lokutan jama’a na gina ramukan tururuwa da kuma cin kwari.
Mazauna jihar Kano na ci gaba da kokawa kan yadda farashin kayan masarufi ke karuwa a kasar.
Daya daga cikin mazauna garin Malam Ibrahim Ahmed, ya ce yanzu abu ne mai matukar wahala ga talakawan Najeriya mazauna jihar su iya cin abinci uku a kullum domin mutane kadan ne ke iya siyan kayan abinci.
Ya bayyana cewa da mafi karancin albashi na N30,000 a halin yanzu, iyali 3 za su iya ciya abinci na mako guda kawai.
“Abin takaici ne ganin yadda kwanan garri ya koma N2,600 maimakon N800 da aka sayar a makon jiya. Garin masara a yanzu ya zama sama da Naira 2,000, kuma wannan shi ne abin da muka sayo Naira 1,200 a da. Batun da ya fi tayar da hankali shi ne yadda farashin ke ci gaba da karuwa a kullum kuma babu wanda ya ke cewa ko yin wani abu a kai.
Ina jin tsoro nan ba da jimawa ba mutane za su fuskanci babban kalubalen yunwa,” in ji shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ziyarar da ta kai wasu kasuwanni a jihar Kano buhun masara mai nauyin kilogiram 100 da ake siyar da shi kan Naira 60,000 a makon jiya yanzu a kai N70,000 zuwa sama; Buhun shinkafar gida 100kg yanzu ya koma N129,000 sabanin N106,000 da aka sayar makwannin da suka gabata.
Haka nan, babban kwandon tumatur da ake sayar da shi kasa da Naira 50,000 a makonnin da suka gabata yanzu N90,000 zuwa N95,000, yayin da buhun barkono ya kai N109,000.
