Connect with us

News

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Binciki Bashin Dala Biliyan 1.5 Da Jihohi 36 Suka Karbo

Published

on

Kungiyar SERAP Ta Bukaci Shugaba Tinubu Ya Binciki Bashin Dala Biliyan 1.5 Da Jihohi 36 Suka Karbo

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kungiyar dake yaki da cin hanci da daidaito na harkokin gwamnati SERAP ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya binciki bashin dala biliyan 1.5 na bankin duniya da jihohi 36 suka karbo tare da babban birnin tarayya.

Kungiyar ta kuma bukaci Tinubu da ya binciki zargin karkatar da lamunin China na $3.121bn da gwamnatin tarayya ta tarba.

Dan Mu Ba Tela Bane Hasali Ma Bai Taba Hawa Keken Dinki Ba —Iyalan Matashin Da DSS Ta Kama

Kungiyar SERAP ta roki Shugaban kasa da ya umarci Babban antoni janar na kasa kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, da hukumomin da suka dace da yaki da cin hanci da rashawa da su gaggauta yin bincike sosai kan yadda aka kashe rancen, ta yadda za a rage “talauci da inganta rayuwar al’umma a fadin jihohin kasarnan.”

Hakan na kunshe ne a wata budaddiyar wasika mai kwanan watan Agusta 10, 2024, mai dauke da sa hannun Mataimakin Daraktan kungiyar, Kolawole Oluwadare.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending