Connect with us

News

Tsoffin Shugabannin Najeriya Buhari Da Jonathan Sun Halarci Taro A Fadar Shugaban Kasa

Published

on

Tsoffin shugabannin Nijeriya, Buhari da Jonathan sun halarci taro a fadar shugaban kasa, VillaAbuja

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jagorancin taron majalisar koli ta farko tun bayan hawansa karagar mulki.

Daga cikin mahalarta taron harda tsoffin shugabannin kasar da suka hada da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan da Yakubu Gowon da kuma Abdusalami Abubakar.

An Daure Direba Shekara 1 A Gidan Yari Bisa Samunsa Da Laifin Satar Litar Man Fetur 1,050.

Sai dai an ruwaito cewar Olusegun Obasanjo bai samu damar halartar taron ba.

Ita dai wannan majalisa ta bai wa shugaban kasa shawara ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da shugabanin majalisun dokoki masu ci da wadanda suka shude da alkalin alkai mai ci da wadanda suka yi ritaya.

Majalisar kan tattauna wasu manyan batutuwa da suka shafi kasa domin bai wa shugaban kasa mai ci shawara a kan yadda zai tinkare su.

Advertisement

Ana saran shugabannin su tattauna batun zanga zangar da matasa suka yi da tsadar rayuwar da jama’a ke fuskanta da kuma halin da kasa ke ciki.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending