Connect with us

News

Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Kama Manyan Jami’an Gwamnatin Jihar, Kan  Badakalar Kudin Magungunan Kananan Hukumomi

Published

on

Ƴan Siyasa Na Haɗa Kai Da Ma’aikata Wajen Wawure Dukiyar Al’umma – Muhyi Magaji

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama manyan jami’an gwamnatin jihar, kan zargin badakalar kudin maganin kananan hukumomi

Cikin jami’an da hukumar ta kama sun hada da babban sakataran ma’aikatar kananan hukumomi Ibrahim Muhammad Kabara, da kuma shugaban karamar hukumar Tarauni, wanda shine shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa reshen jihar Kano (ALGON) Abdullahi Ibrahim Bashir, da Kuma wasu mutane biyar, da ake zarginsu da hannu a badakalar kwangilar magungunan kananan hukumomi 44.

Advertisement

Akwai Barazanar Fuskantar Ambaliyar Ruwan Sama A Kano –Hukumar  NiMet

Kazalika hukumar ta aike da takardar gaiyata ga shugaban rukunin shagunan magani na NOVEMED, wanda ‘da ne wurin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.

Hukumar na tuhumar wadannan mutane da sabawa dokokin tsarin aikin gwamnati, ta hanyar aiwatar da kwangilar da bata cika ka’ida ba, ba tare kuma da sahalewar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba.

Advertisement

Jaridar Solacebase ta rawaito wata majiya na cewa, tuni shugaban ALGON Kuma shugaban karamar hukumar Tarauni, ya amsa laifin sa, Inda ya tabbatar da cewa, ya bayarda da umarni ba bisa ka’ida ba, na biyan sama da naira millyan 402 cikin kudaden siyan magunguna ga kananan hukumomin jihar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending