Connect with us

News

Ruwan Sama Ya Lalata Gidaje, Makarantu Da   Wurare Kasuwancin A Zariya

Published

on

images (8)

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rahotanni na nuni da cewa ruwan sama yayiwa  mazauna garin Chikaji da ke karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna sun yi kira da a kawo musu dauki bayan da wata ambaliyar ruwa ta lalata makabarta, gidaje da dukiyoyi a yankin.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, ambaliyar ta afku a yankin ne a ranar Litinin din da ta gabata sakamakon mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i bakwai ana yi daga karfe 5 na safe zuwa karfe 1 na rana.

Matsalar tsaro: Kungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da kama wani Matashi sabida wallafa wani faifan bidiyo

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Talata a Zariya, Hakimin kauyen Chikaji, Auwal Sani-Dambaba, ya ce ambaliyar ta shafi gidaje sama da 200 a yankin.

Ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da wasu sassa na makarantar firamare ta LEA tare da lalata wani muhimmin bangare na makabartar Ojo.

“A halin yanzu, wadanda abin ya shafa sun samu mafaka ne a makwabta amma ba a samu asarar rai ba a lokacin da lamarin ya faru. Sai dai kuma an bar kaburbura da yawa a bude,” in ji shugaban kauyen.

Advertisement

Yayin da yake kokawa kan wannan mummunan lamari, hakimin kauyen ya ce kwana daya da sa’o’i bayan ambaliyar, babu wani tallafi ko taimako daga gwamnati daga jiha ko daga

Abuja.

A wani mataki na tunkarar kalubalen da ya fuskantar makabartar, babban limamin masallacin Chikaji, Suleiman Liman, ya ce al’ummar yankin sun kira taron gaggawa na masu hannu da shuni a yankin.

Liman ya ce taron gaggawar zai kuma duba halin da wadanda ambaliyar ta shafa ke ciki.

Ibrahim Ahmed, wanda aka hange a tsaye a cikin gidansa da ke zube a kasa ya ce sun godewa Allah da aka yi ambaliyar ruwa da rana. Ya ce da dare ne da ba san irin asarar da za a ayi ba.

Kakakin majalisar Wakilai, wanda ɗan asalin yankin Sabon Gari ne, umarci hukumar bada agajin gaggawa ta Kasa NEMA, ta gaggauta kaiwa mutanen da abin ya shafa ɗauki, sannan kuma ya yi kira da mazauna yankin su rika ɗaukar matakai domin gujewa afkuwar irin haka.

Advertisement

Ya ce ‘yan gidan nasa suna kwashe ruwa a gidan, sai wani sashe na gidan ya rufta, ya kara da cewa, “Ban cire komai daga gidan ba, domin na shagaltu da kare ‘ya’yana daga baraguzan ginin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending