Connect with us

News

Yan Najeriya 400 Da Aka Ta Tiso Ƙeyar Su Daga Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Isu Filin Jirgin Saman  Abuja

Published

on

Yan Najeriya 400 Da Aka Ta Tiso Ƙeyar Su Daga Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Isu Filin Jirgin Saman  Abuja

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA

Mahukuntan Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa sun tiso keyar ƴan Najeriya 400 sakamakon zama a ƙasar ta yankin gabas ta tsakiya ba bisa ka’ida ba, matakin da ke zuwa makwanni bayan dawo da bayar da biza da ƙasar ta yi ga al’ummar Najeriya.

Advertisement

Rahotanni sun ce manyan hukumomin ƙasar da suka haɗa da na agaji da mai kula da ƴan cirani da masu kula da shige da fice da kuma hukumar yaƙi da safarar mutane baya ga jami’an ofishin babban mai bayar da shawara kan sha’anin tsaro na Najeriyar ne suka tarbi mutanen a filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriya.

Gwamnatin Kano Ta Dakatar Da Tsawaita Wa’adin Ma’aikan Jihar 4,000 Da Ganduje Ya Yi

Kamar yadda kafofin yaɗa labaran Najeriyar suka ruwaito, mutanen 400 sun ƙunshi mata 90 da kuma maza 310 waɗanda bayanai suka ce wasunsu izinin zamansu a ƙasar ta Haɗaɗɗiyar daular Larabawa ya ƙare amma suka ƙi ficewa yayinda wasunsu suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

Galibi ƴan Najeriyar kan yi amfani da damar shiga ƙasar da nufin karatu ko kuma cinikayya amma sai su juye zuwa ƙwadago ba tare da takardun izinin yin aiki ba.

Haka zalika akwai bayanan da ke alaƙanta ƴan Najeriyar da aikata ba dai dai ba a ƙasashen musamman na gabas ta tsakiya lamarin da a lokuta da dama kan kaiwa ga korosu gida.

Advertisement

Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙasashe ke tiso ƙeyar ƴan Najeriyar ba, domin kuwa ko a Juma’ar da ta gabata sai da Turkiya ta kwaso ƴan Najeriyar 103 tare da miƙasu ga hukumar NEMA, yayinda ko a karshen shekarar bara, Saudiya ta tiso ƙeyar ƴan Najeriya 264 zuwa gida bayan da ta soke bizar su jim kaɗan bayan saukarsu a filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz da ke birnin Jidda.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending