News
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗin Sake Samun Mummunar Ambaliyar Ruwa A Jihohin Najeriya Biyu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ministan Albarkatun ruwa da tsaftar muhallai a Najeriya, Joseph Utsev ya yi gargaɗin sake samun mummunar ambaliyar Ruwa a kogunan Neja da Benue.
Yayin da yake jawabi ga taron menama labarai a Abuja, Ministan ya ce an samu ƙaruwar ruwan da ke ƙwarara a kogunan biyu zuwa yankin Naija Delta da ke kudancin Najeriya.
Yadda CBN Ya Ƙaƙaba Wa Masu POS Ƙa’idoji Da Dabaibayin Yin Hada-hadar Kuɗaɗe
‘A yayin da muke jajanta wa al’ummomin jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Bauchi da sauran jihohin da suka fuskanci ambaliyar Ruwa, muna ƙara jan hankalin ‘yan ƙasar game da yiwuwar sake fuskantar wata ambaliyar daga kogunan Benue da Neja da wasu yankunan yankin”, in ji ministan.
Kan haka ne mista Utsev ya yi kira ga mazauna yankin su ɗauki matakai domin kauce wa bala’in ambaliya a wasu sassan kudancin ƙasar.
Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar birnin Maiduguri ke fuskantar mummunar ambaliya da ta auka wa birnin sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin.
PRNIGERIAN ta ruwaito cewa Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ya ce lamarin ya shafi kusan mutum miliyan biyu.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
