News
Ana Fargabar Mutuwar Mutane 64 Bayan Kifewar Kwale-kwale A Zamfara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ana fargabar mutuwar mutane 64 bayan kifewar kwale-kwale da suke ciki ranar Asabar a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara dake Najeriya, kasancewar mutane 6 kacal aka samu damar cetowa daga cikin 70 din da suka dulmiye a cikin ruwan.
Shugaban karamar hukumar ta Gummi Aminu Nuhu Falale, ya ce kwale-kwale na dauke da manoma 70, a kan hanyarsu ta zuwa gonakinsu da safiyar Asabar, to amma ma’aikatan agaji sun samu nasarar zakulo 6 a raye, sannan kuma suna ci gaba laluben sauran wadanda suka nutse a cikin ruwan.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗin Sake Samun Mummunar Ambaliyar Ruwa A Jihohin Najeriya Biyu
Kimanin kusan manoma dubu daya ne ke jigilar zuwa gonakinsu ta wannan yanki a kullum rana, to amma kwale-kwale ruwan guda biyu ne kacal suke amfani da su domin wannan zirga-zirga, lamarin da ke janyo cikar jiragen ruwan fiye da kima a duk lokacin da suke tafiyar, kamar yadda wani mai rike da sarautar gargajiya na yankin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
