Connect with us

News

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayar Da Umarnin Rufe Hanyar Buk Road Ranar Alhamis

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano Ta Bayar Da Umarnin Rufe Hanyar Buk Road Ranar Alhamis

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka da gidaje na sanar da al’umma cewa ta bayar da umarnin rufe hanyar titin Jami’ar Bayero (BUK ROAD) tsakanin ƙofar Kwalejin Rumfa zuwa gidan Mai na Aliko.

Advertisement

Arewa Radiyo ta ruwaito cewa saboda haka ne ake sanar da al’ummar jihar Kano cewa, za a rufe wannan ɓangare daga ranar Alhamis 19 GA watan da muke ciki.

Aƙalla Mutum 40 Ne Masu Mauludi Suka Rasu Sanadiyyar Haɗarin Mota 

Bisa buƙatar sauƙaƙq zirga-zirga, ma’aikatar ayyuka da gidaje ta jihar Kano ta samar da hanyoyin da za a yi amfani da su domin kaucewa wajen aikin da za a rufe.

Advertisement

Matafiya waɗanda suka fito daga ɓangaren Ƙofar Gadon Ƙaya, za su iya bin hanyoyin ratse da suka haɗa da:

– Titin bayan ofishin AIG gidan Mai na Azman zuwa Sharaɗa

Advertisement

– Titin Ƙofar Na’isa zuwa cikin gari

 

Advertisement

– Sabon titin ratse da aka samar tun daga ƙarshen titin katangar filin wasanni na Mahaha zuwa dab da gidan Mai na A.A Rano da ke kan titin Sharaɗa.

-Masu ababen hawa daga bangaren gidan Murtala kuma za su iya bin titin Lawan Dambazau, titin Sabuwar Kofa, da kuma titin yanke da aka samar da ke cikin Kwalejin Rumfa (Rumfa College).

Advertisement

Ana shawartar masu ababen hawa da su nisanci wajen da ake gudanar da wannan aiki idan ba ya zama dole ba, domin rage cunkoso da zirga-zirga cikin tsanaki.

Hakan na kunshe cikin wata Sanarwa da Kwamishinan ayyuka da gidaje na jihar Kano

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending