Connect with us

News

Ambaliyar Ruwa:  Majalisar Wakilai Ta Yi Watsi Da Ƙudirin Tallafin N300bn Ga Al’ummar Maiduguri

Published

on

Mutum 259 ne suka mutu yayin da 625,239 suka rasa matsugunansu a ambaliyar ruwa a Nijeriya – NEMA

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Majalisar Wakilai ta kasa Najeriya ta yi watsi da ƙudirin neman tallafi na musamman na Naira biliyan 300 daga gwamnatin tarayya domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri dake jihar Borno.

Matakin dai ya biyo bayan gyare-gyaren ƙudirin da gwamnatin tarayya ta yi na ganin an shawo kan matsalar ambaliyar ruwa ga mazauna Borno da kewaye.

A zaman Majalisar ranar Laraba, Amos Magaji, wakilin mazabar Jaba/Zangon Kataf na tarayya, ya gabatar da wani ƙudiri mai matukar muhimmanci ga al’umma, inda ya bayyana irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi wa gidaje da kasuwanni da cibiyoyin kiwon lafiya da dama.

ƘUDIRIN INUWA GARBA

Yayin da Inuwa Garba, Wakilin Mazabar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, ya gabatar da ƙudirin neman tallafin Naira Biliyan 300 don tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma rage radadin da al’umma suka shiga.

Advertisement

Duk da cewa daidaikun mutane na bada gudunmawa, wanda abin yabawa ne, ya kamata gwamnatin tarayya kuma ta ware tallafi na musamman na kusan Naira biliyan 300 domin taimawa wadanda lamarin ya shafa a Borno,”

 

ƘIN AMINCEWA DA ƘUDIRIN

Sai dai a lokacin da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya bukaci a kada kuri’a kan gyaran, daga karshe ‘yan majalisar suka kada kuri’ar kin amincewa.

A maimakon haka, majalisar ta karfafawa gwamnatin tarayya gwiwa da ta taimaka wa wadanda abin ya shafa gwargwadon iko, ba tare da tantance adadin kudi ba.

ABIN DA SUKA AMINCE

Advertisement

Haka kuma ta bukaci ma’aikatar lafiya ta tarayya da ta shiga tsakani domin dakile barnar da ambaliyar ruwa ta yi a asibitin koyarwa na Maiduguri da sauran cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.

Majalisar ta bukaci ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya da ta gaggauta maido da wutar lantarki a asibitin tare da daukar karin matakan dakile illar bala’in.

‘Yan majalisar dai sun bukaci gwamnatin tarayya da ta fadada taimako zuwa ma’aikatan gidan gyaran hali na Najeriya wadanda ambaliyar ruwan ta shafa.

 

FRI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending