News
Tankar Man Fetur Ta Sake Fashewa Ya Yin Da Mutane Suka Jikkata Gidaje Da Motoci Suka Kone
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata tankar man fetur da ta yi hatsari da sanyin safiyar Laraba ta kona gidaje da motoci tare da jikkata wasu mutane biyu a garin Ibafo da ke karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar Ogun a ranar Laraba.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa, tankar man fetur ta kama da wuta ne a wani gari da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Ana Tsaka Da Jiran Dawowar Shugaba Tinubu Najeriya Shettima Zai Dage Zuwa Kasar Sweden
Shedun gani da ido sun ce, tayar tankar ce ta fashe, wanda hakan ya yi sanadin faduwar motar .
Tankar ta fashe bayan faduwa inda ta lalata gidaje da ababen hawa da ke kusa da wurin, inji wani ganau.
Akalla motoci biyar da suka hada da manyan motoci sun lalace yayin da wasu mutane biyu suka samu raunuka.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a Abeokuta, Kakakin hukumar kiyaye hadurra ta jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya ce, ba a samu asarar rai ba a lamarin.
