News
Fubara Ya Amince Da Biyan Mafi Karancin Albashi Na N85,000 Ga Ma’aikatan Jihar.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin jihar Ribas Siminalayi Fubara ya amince da biyan mafi karancin albashi na N85,000 ga ma’aikatan jihar.
Shugaban ma’aikata na jihar, George Nwaeke, ya sanar da cewa Gwamna Siminalayi Fubara ne ya amince da hakan yayin wata ganawar sirri da shugabannin kwadago da manyan jami’an gwamnati.
Hukumar Hisbah Ta Kama Kwamishina Bisa Zargin Sa Da Lalata Da Matar Aure A Kano
Bayan taron, Nwaeke ya tabbatar da cewa aiwatar da sabon mafi karancin albashin zai fara aiki nan take.
A nasu bangaren, Shugaban Kungiyar Tattaunawar ta hadin gwiwa, Chukwu Emecheta ya yabawa Gwamna Fubara bisa biyan bukatun ma’aikatan Jihar Ribas.
Ya nuna jin dadinsa ga jajircewar da Gwamnan ya yi ga ma’aikata.
Shima da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya NLC a jihar Ribas, Alex Agwanwor, ya bayyana cewa mafi karancin albashin zai taimaka matuka wajen rage wahalhalun tattalin arziki da ma’aikata ke fuskanta a jihar.
