News
Ana Zargin Miji Da Kone Matarsa Da Fetur Akan Sabani
DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wani mutum mai shekaru 55 mai suna Olubunmi Johnson, ya shiga hannun ‘yansandan Jihar Ogun, bisa zargin kone matarsa da wuta a yankin Ota.
LEADERSHIP HAUSA ta ruwaito cewa lamarin ya faru misalin karfe 8:30 na daren ranar Juma’a, bayan wata sabani ya barke tsakanin ma’auratan a gidansu da ke kan titin Fagbuyi, Ilogbo.
Ana zargin Johnson da zuba wa matarsa mai suna Kikelomo fetur sannan ya cinna mata wuta.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin.
Ta ce iyalan matar sun sanar wa ‘yansanda faruwar lamarin.
Odutola ta kara da cewa, duk da har yanzu ba a san musabbabin sabanin ba, amma an garzaya da matar asibiti.
Ta bayyana cewa an kama Johnson, kuma ‘yansanda na bincike kan lamarin a matsayin yunkurin kisa.
“Jami’an ‘yansanda daga ofishin Ilogbo sun yi gaggawar daukar mataki, inda suka kama wanda ake zargi mai shekaru 55.
“Shaidu sun garzaya da matar zuwa asibiti bayan ya cinna mata wuta,” in ji Odutola.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
