News
Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Tsakaninta Da Hezbollah A Lebanon
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar Hezbollah.
Netanyahu ya bayyana haka ne bayan da ya jagoranci taron majalisar ƙolin Isra’ila ta tsaro akan tayin yarjejeniyar tagaita wutar a Lebanon da masu shiga tsakanin a ƙarƙashin jagorancin Amurka suka gabatar masa.
Kungiyar MATAN ta Kaddamar da raban Shinkafar Gwamnatin Tarayya Kan N40,000 A Kano
Firaministan ya ce yarjejeniyar tsagaita wutar da aka daɗe ana dakon ganin an ƙulla ba za ta fara aiki ba, har sai majalisar ministocinsa ta amince da ita.
Sai dai wani abu da ya ja hankali, wanda kuma za a iya cewar ya haifar da fargaba akan makomar yarjejeniyar da tsagaita wutar shi ne gargaɗin da Netanyahu yayi kan cewa Isra’ila na da damar janyewa daga yarjejeniyar idan buƙatar hakan ta taso domin kare kanta daga duk wani lamari da ka iya kasancewa babbar barazana gareta.
Wannan ci gaba da aka samu na zuwa a yayin da Isra’ilar ke ci gaba da ɓarin wuta a sassan Lebanon da zummar neman murƙushe mayakan Hezbollah, lamarin da ya sanya ƙaruwar adadin mamata da kuma waɗanda suka jikkata a ƙasar.
Ma’aikatar lafiyar Lebanon ta ce ya zuwa ranar Lahadin da ta gabata, mutane fiye da dubu 3 da 750 Isra’ila ta kashe, baya ga jikkata wasu kimanin dubu 15,630 akasarinsu mata da yara, a hare-haren da take ci gaba da kai wa da sunan murƙushe ƙungiyar Hezbollah.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
