Connect with us

News

Jami’an Hukumar DSS Sun Saki Dan Fafutukar Kare Dimokradiyya Zubair A. Zubair 

Published

on

Jami'an Hukumar DSS Sun Kama Wani Mai Fafutukar Kare DimokradiyyaZubair A Kano

DAGA NUSIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Jami’an Hukumar DSS ta saki Zubair, wanda ya kafa  ƙungiyar gwagwarmayar dimokuradiyya, wato Take-It-Back Movement (TIB) a Jihar Kano, wanda aka kamashi a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana cewa an saki Zubair a Abuja da daddare ranar Juma’a, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Kano.

Makarantar Madarasatul Ajyalul Mustaqbal Litahfizil Qur’an Waddirasatil IslamiyyA Za Tayi Bikin Saukar Karatun Alqur’ani Ga Dalibanta

Sai dai jami’an DSS sun riƙe wayarsa, wadda har yanzu ba a mayar masa da ita ba.

“An saki Zubair jiya da daddare a Abuja. Yana kan hanyarsa ta zuwa Kano a halin yanzu. Amma har yanzu suna riƙe da wayarsa,” in ji wata majiya.

Ƙungiyar TIB, wadda ita ce ta fara bayyana labarin kama Zubair, ta ce dalilan kama shi bai fito fili ba.

Advertisement

Sai dai wasu majiyoyi sun ce an kama shi ne saboda wani rubutu da ya yi a Facebook da ake zargin ya soki gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ana yawaitar tsangwamar masu sukar gwamnati a Najeriya daga masu riƙe da muƙamai a matakai daban-daban na ƙasa.

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin shugabancin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, tana fuskantar zarge-zargen tsangwamar ‘yan gwagwarmaya, ‘yan jarida, da kuma waɗanda ke sukar hukumomi.

 

KANO TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending