News
Karamin Ministan Man Fetur Da Iskar Gas Ya Yabawa NNPC Bisa Aikin Cibiyar Samar Da Wutar Lantarki Dake Maiduguri
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Karamin ministan albarkatun man fetur da Iskar Gas Rt. Hon. Ekperikpe Ekpo ya yabawa kamfanin NNPC bisa nasarar aiwatar da manufofin shugaban kasa ta
hanyar samar da ayyuka masu tasiri ga ‘yan kasa.
Wannan katafaren aiki guda ne cikin ire iren ayyuka samar da wutar lantarki na gaggawa dake Maiduguri (MEPP) wanda Shugaban kasa Bola Tinubu ta kaddamar domin amfanar ‘yan kasa.
Ba mu nemi Jonathan don yi mana takara a 2027 ba — Jam’iyyar PDP
Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a cibiyar samar da lantarkin ranar Asabar, 14 ga watan Disamba, 2024.
Ministan wanda ya samu rakiyar shugaban rukunin kamfanin NNPC Ltd., Mele Kolo Kyari, da mataimakin shugaban kasa, da sauran masu ruwa da tsaki na kamfanin NNPC.
Ita dai cibiyar samar da lantarkin MEPP wani aikin hadakar wutar lantarki ne mai karfin megawatt 50 da aka kaddamar a ranar 2 ga Maris, 2023.
Rahotonni sunce tuni an riga an kammala aikin 32MW na aikin kuma tuni ya fara aiki, yayin da sauran Megawatt 18MW zai fara aiki cikin shekarar 2025 dake karatowa.
