Connect with us

News

Majalisar Zartarwa Ta Amince Da Naira Tiriliyan 47.9 A Matsayin Kasafin Shekarar 2025  

Published

on

Majalisar wakilai ta ce gwamnonin na barazanar hana mambobinta takara a 2027 matukar suka goyi bayan dokar haraji ta Tinubu

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da kasafin kudin shekarar 2025, wanda shugaba Tinubu zai gabatarmata.

 

Advertisement

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala taron majaliar zartarwa a fadar shugaban Najeriya, a yau Litinin, ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu, ya ce kasafin kuɗin na 2025, an yi hasasshen za a kashe kusan naira tiriliyon 48.

 

Advertisement

Ministan ya ce an yi kasasfin kudin ne kan farashin gangar mai dallar Amurka 75, tare da samar da gana sama da miliyan biyu duk rana, yayin aka yi hasashen farashin dalar Amurka kan naira 1,400.

 

Advertisement

Bugudu  ya ce kuma an yi hasashen kuɗin shigar ƙasar kan kusan naira tiriliyon 35 kamar Yadda BBC Hausa ya rawaito

 

Advertisement

Akwai alamun dake nuna cewa shugaba Tinubu ba zai gabatar da kasafin kuɗin gaban Majalisar Dokokin ƙasar a gobe Talata ba kamar yadda aka tsara tunda farko.

 

Advertisement

Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammed Idris ya ce shugabannin majalissun da ɓangaren zartarwa na aiki tare domin samar da ranar da za a gabatar da ƙudurin.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending