News
Kotu Ta Bayar Da Belin Matar Da Tayi Barazanar Kashe Dan Shugaban Kasa Tinubu, Da Shugaban Yan Sanda
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da beli na Naira miliyan 10 ga Olamide Thomas, wata yar gwagwarmaya da ake zargi da yin kalaman kazafi kan dan gidan shugaban kasa, Seyi Tinubu a kafar sada zumunta.
An kuma bukaci Thomas ta gabatar da mai tsaya mata.
“Na yi nazarin shaidun rantsuwa daga bangaren wanda ake tuhuma da kuma na mai kara,” in ji shi.
Alkalin ya bukaci mai tsaya mata ya gabatar da takardar bayanan kadarorin sa tare da gabatar da takardar shaidar biyan haraji na tsawon shekaru uku.
Ya kuma bayyana cewa dole ne mai tsaya mata ya zama mazauni ne a cikin yankin da kotun ke da hurumi kamar yanda Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito
Advertisements
