Connect with us

News

Kwamishinan Yada Labarai Ya Gana Da Shuwagabannin Hukumomin Dake Karkashin Ma’aikatar Sa

Published

on

Har Yanzu Amb. Ibrahim Waiya Ne Shugaban Gamayyar Kungiyoyi Masu Zaman Kansu A Kano

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, a karon farko ya gana da ma’aikata da Shuwagabannin sassa na ma’aikatar domin sanin ayyukansu da kuma tattauna hanyoyin inganta aiyukansu.

Advertisement

A yayin taron, Daraktocin sun ba da cikakkun bayanai game da jadawalin ayyukansu a sassa daban-daban tare da bayyana muhimman abubuwan da ke bukatar kulawa don inganta ayyuka.

Hukumar ICPC Ta Gurfanar Da Tsohon Hadimin El-rufa’i A Gaban Kotu Bisa Zargin Almundahana

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da daraktan aiyuka na musamman na ma’aikatar Sani Abba Yola ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

Advertisement

Da yake jawabi yayin taron, Kwamishinan ya sake nanata kudurin sa na sauya fasalin ma’aikatar ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa, da tabbatar da ma’aikatar ta na gudanar da aiyukanta daidai da tsarin da kasashen da suka ci gaba suke kai.

Kwamared Waiya ya jaddada kudirinsa na inganta jin dadain ma’aikatan Ma’aikatar dake aiki ko ina a ma’aikatu da hukumomi da kuma kananan hukumomi jihar Kano.

Advertisement

Ya kuma yi alkawarin ba da fifiko waje bayar da horo ga ma’aikata don baiwa ma’aikata damar samun dabaru na zamani domin yada manufofin gwamnati da tsare-tsarenta .

Bugu da kari, Kwamishinan ya tabbatar wa ma’aikatan cewa za a samar da kayan aiki masu mahimmanci don inganta aiki.

Advertisement

Hakazalika, Kwamishinan ya yi wata ganawa ta daban da shugabannin hukumomin da ke karkashin ma’aikatar domin inganta alaka.

A yayin taron, kowane daga cikin Shugabannin hukumomin ya yi bayanin nasarorin da suka samu tare da bayyana wuraren da ake bukatar ma’aikatar ta sa hannu domin cimma manufofinsu.

Advertisement

Shugabannin hukumomin da suka halarci taron sun hada da manajan daraktan gidan rediyon Kano, Adamu Abubakar Rano; Manajan Daraktan Kamfanin Buga na Kano, Yahaya Muhammad Idris, Manajan Daraktan Kamfanin Bugawa na Triumph, Muhammad Hamisu Abdullahi Manajan Daraktan Hukumar Tace Tace Abba El-Mustaph; da kuma Manajan Daraktan Gidan Talabijin na Abubakar Rimi. Hauwa Isa Ibrahim

A jawabinsa babban sakataren ma’aikatar Adamu Bala Muhammad ya baiwa kwamishanan tabbacin ma’aikatan za su ba shi goyon baya domin ganin ya samu nasarar jagorantar ma’aikatar domin samun nasarar aikin ta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending