Connect with us

News

AIKIN TITIN JIRGIN KASA : Ya Kamata Gwamnatin tarayya ta biya diyar gidaje Da Gonakin Da Aikin Rutsa Dasu A Kano 

Published

on

IMG 20250121 WA0015

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gamayyar al’ummar garin Rimin zakara da ke cikin karamar hukumar Ungoggo a nan kano, sun bukaci Gwamnanatin tarayya sa sauran wanda abin ya Shafa da su duba halin da al’umma suke ciki samakon aikin titin jirgin kasa da ya rutsa gidajensu da gonakinsu wanda hukuma tsahon lokaci ba’a kai ga biyansu ba.

Shugaban gamayyar Malam Hassan Rimin zakara ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gudana a yau.

Ya kara da cewa wasu anyi musu rusau basu gyara gidajensu ba, kuma an ce duk wanda yayi aiki a ciki yayi aikin banza.

Hukumar Kula Da Aikin Hajji Ta Najeriya Ta Sanar Da Kudin Aikin Hajjin Bana

Sama da shekara guda kenan hukumomin da ke kula da lamarin suka sanya dokar cewa kada mu yi aiki a ciki kuma duk mun hakura.

Shugaban gamayyar ya kara da cewa Babban abinda ya basu mamaki ma shi ne, tu ni aka biya ‘Yan Yamma damu da Kuma ‘Yan gabas damu mu kuma a tsakiya muke a cewar sa.

Advertisement

Ya Kuma ce idan aka ce sai damuna za’a biya mu to a wannan lokacin za’a tashi hankalin da mu da iyalanmu musamman ma ganin cewa marasa karbi ne da yawa a cikin mu.

Malam Hassan ya Kuma bukaci Sarkin Kano da majalisar dokokin Jihar Kano data sanya baki a lamarin.

Shima da yake jawabi Yaro Sabi’u Rimin zakara shi ne Sakataren Gamayyar kira ya yi ga Gwamnan kano da sauran masu ruwa da tsaki dasu sanya baki domin kawo musu dauki.

 

Ya kara da cewa a halin yanzu komai yayi tsada wanda koma an basu wannan diya kamar yadda aka baiwa makotansu abin ba zai wadatar dasu ba, kasancewar komai yayi tashin gwauron zabi a halin yanzu.

Sakataren ya kuma ce, da yawa daga cikin su abincin da za su ci gagararsu yake balle mahallinsu.

Advertisement

Ya Kuma godewa Gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmad Tunibu bisa nuna kulawar sa ga al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending