Connect with us

News

Wata Sabuwar Gobarar Daji Ta Tashi A Jihar California

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumomi a California sun ba da sanarwa ga al’ummomin da ke daura da Castaic Lake da su fice daga yankin, bayan da wata sabuwar gobarar daji ta tashi a tsaunukan arewacin Los Angeles.

Advertisement

Kudancin California yana fama da tashin gobara saboda busasshiyar Iska da rashin samun ruwan sama.

Al’ummar Dawakin Tofa Mun amince Sunusi Bature ya fito takarar majalisar tarayya–Hon. Mai Kaza 

Sannan hukumomi sun yi kira ga al’ummar yankin da su kaurace wa kusa da yankin saboda shakar gurbataccen hayaki.

Advertisement

A halin da ake ciki, akwai gargadi game da yiwuwar tashin wata mummunar gobarar a kudancin California.

Dr. Talatu Bako ‘yar Najeriya da ke zaune a Los Angeles, California ta shaida wa Muryar Amurka cewa gobarar ta yankin Castaic Lake ta yi barna sosai, kuma hukumomin kashe gobara su na ta fafatawa wajen shawo kanta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending