News
An Tsinci Jariri A Cikin Kwali A Unguwar Tudun Murtala Tagarji A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A safiyar ranar Asabar, al’ummar unguwar Tudun Murtala Tagarji dake Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano sun wayi gari da abun mamaki bayan an tsinci wani jariri da aka haifa an jefar a cikin kwali.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na dare a bakin ramin Kaura, inda ‘yan bijilante na Operation Zaman Lafiya, karkashin jagorancin Commander Sulaiman Rabiu, suka ci karo da jaririn yayin gudanar da sintirinsu na tsaro.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa jaririn yana cikin kwali a wajen da ba kowa, wanda hakan ke nuna cewa an jefar da shi cikin dare.
Bayan tabbatar da cewa yana numfashi, jami’an tsaron sun dauke shi zuwa wurin da ya dace domin samun kulawa.
Har zuwa yanzu, ba a gano waye ya jefar da jaririn ba, amma hukumomi na ci gaba da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan abin takaici.
Al’ummar yankin sun bayyana damuwarsu, tare da kira ga iyaye da su rika tausaya wa rayukan da suka haifa.
