Connect with us

News

Wani Jariri Ya Mutu A Cikin Jirgin Air France

Published

on

FB IMG 1771883508797

Wani jariri da ke fama da matsananciyar cutar zuciya ya rasu a cikin jirgin saman Air France yayin da ake kan hanya daga Nairobi na ƙasar Kenya zuwa Paris a Faransa domin neman kulawar likitoci.

Rahotanni sun bayyana cewa an garzaya da jaririn zuwa Faransa ne domin samun kulawar gaggawa sakamakon wata mummunar cutar zuciya da yake fama da ita. Sai dai duk da kokarin da ma’aikatan lafiya da ke cikin jirgin suka yi na ceton rayuwarsa, jaririn ya rasu bayan ya samu matsananciyar matsalar numfashi.

Advertisement

Jarumin Barkwanci Rajpal Yadav Ya Dawo Bakin Aiki Bayan Fitowa Daga Kurkuku Saboda Bashi

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, inda aka ce jaririn ya gamu da bugun numfashi (respiratory arrest) a cikin jirgin, lamarin da ya sa aka yi kokarin gaggawa domin farfado da shi, amma abin ya ci tura.

Advertisement

Wannan lamari ya sake jaddada irin kalubalen da ake fuskanta wajen kula da marasa lafiya masu tsananin bukatar agajin gaggawa yayin tafiyar jirgin sama, musamman idan suna cikin mawuyacin hali tun kafin tafiya.

Har yanzu hukumomin jirgin sama da na lafiya ba su fitar da cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru ba, yayin da ake sa ran karin bayani daga bangarorin da abin ya shafa.

Advertisement

 

 

Advertisement

LE PARISIEN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending