News
Ma’aikatar Gine-gine Ta Najeriya NIOB Ta Karrama Ma’aji Sumaila da Lambar Girmamawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Yadda Ake Ba da Kwangiloli da Bibiyar Ayyuka na Jihar Kano, Comrade Nura Ma’aji Sumaila, ya samu lambar yabo ta musamman daga Nigerian Institute of Building (NIOB) reshen Kano.
Wannan karramawa na da nufin jinjinawa gudunmawar da ya bayar wajen inganta harkar gine-gine, musamman a fannin kula da ayyukan gwamnati tun bayan nadinsa a mukamin.
Da yake gabatar da kyautar, wakilin NIOB ya bayyana cewa hukumar tana da al’adar girmama mutanen da ke bayar da gudunmawa a fannin gine-gine. Ya ce: “Ta wannan lambar yabo, muna karrama nagarta da irin tasirin da ake samu a bangaren gine-gine.”
A nasa jawabin bayan karbar lambar yabon, Ma’aji Sumaila ya nuna matukar godiya ga NIOB bisa wannan girmamawa. Ya ce: “Wannan karramawa shaida ce ta jajircewarmu. Ina tabbatar muku da cewa ma’aikatar mu za ta ci gaba da yin aiki tare da NIOB domin tabbatar da bin ka’idojin aikin gine-gine.”
Wannan karramawa ta biyo bayan jagorancin kwamishinan na kwamitin mutum shida da Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya kafa don duba ci gaban aikin gina dakunan karatu na Kwankwasiyya Gida-Gida a duk kananan hukumomi 44 na jihar. Kwamitin ya kammala zagayensa kuma yana shirin gabatar da rahoto ga gwamnan domin ɗaukar matakan da suka dace.
