News
Gwamnatin Borno Ta Hana Malami Albashin Watanni 20 Duk Da Wanke Shi Daga Zargi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani malamin makaranta a jihar Borno, Hassan Bukar, ya bayyana yadda ya shafe watanni 20 ba tare da karbar albashi ba, duk da cewa an wanke shi daga zargin kin zuwa aiki ba tare da izini ba.
Bukar, malamin Turanci a makarantar GSS Damasak, ya ce an dakatar da albashinsa ne bayan an zarge shi da kin zuwa aiki na tsawon makonni uku, alhali yana kula da matarsa a asibiti wacce ke fama da rashin lafiya.
Hukumar PCACC Ta Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma kan zargin badakalar filin N100m a Kano
A hirarsa da WikkiTimes, Bukar ya ce ya sanar da shugaban makarantar, Alhaji Shettima Ali, halin da yake ciki, amma sai aka mika sunansa ga ma’aikatar ilimi bisa zargin kin zuwa aiki da gangan.
Duk da haka, bayan an sallame su daga asibiti, ya rubuta takardar neman afuwa tare da komawa bakin aikinsa, amma har yanzu ba a dawo masa da albashinsa ba.
An Wanke Shi Amma Har Yanzu Ana Rike Albashinsa
Bayan dogon bincike, an wanke Bukar daga duk wani zargi, inda har aka yaba da kokarinsa a matsayin daya daga cikin kwararrun malamai a makarantar.
Sai dai duk da haka, gwamnati ta gaza dawo masa da albashinsa ko ci gaba da biyansa.
“Na rubuta takardu da dama domin a dawo da albashina, amma har yanzu babu labari,” in ji Bukar.
Hana Malamin Gani Kwamishina
Bukar ya ce lokacin da kwamishinan ilimi ya ziyarci makarantar, ya yi masa alkawarin duba matsalarsa tare da ba shi tallafi kan matsalar idonsa.
“Kwamishinan ya bukace ni da in same shi a ofis, amma duk yunkurina na ganinsa ya ci tura. Har yanzu ana hana ni shiga ofishinsa,” in ji malamin.
Martanin Hukumar Ilimi
Hukumar Kula da Malaman Makaranta ta jihar Borno ta karyata zargin cewa tana dakatar da albashin malamai saboda kin zuwa aiki na makonni uku kawai.
Mai magana da yawun hukumar, Zara Aji Monguno, ta ce ana dakatar da albashi ne kawai idan malami ya ki zuwa aiki na tsawon wata guda ko fiye ba tare da izini ba.
Ta ce sabon shugaban hukumar ya fara duba matsalolin malamai da aka dakatar da albashinsu tun daga 2020, kuma wasu sun fara karbar albashinsu.
Sai dai Bukar ya dage cewa ya bi duk matakan da suka dace, amma har yanzu ba a dawo da hakkinsa ba.
“Ba na jin tsoron abin da zai biyo baya. Ni mai iyali ne kuma rayuwa ta yi tsanani. Ina rokon gwamnatin Borno ta taimaka a dawo
min da albashina,” in ji malamin.
