Connect with us

News

Dalibai Sun Lakada Wa Malami Duka Akan Hana Su Satar Jarrabawa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Akalla wasu dalibai 10 ne aka samu rahoton sun lakada wa malaminsu dukan tsiya saboda hana su satar jarrabawa a makaranta a  Jihar Ogun.

Advertisement

Rahotanni na nuni da cewa, lamarin ya faru ne ranar Talata a wata makarantar sakandire ta Isanbi Comprehensive High School da ke Karamar Hukumar Ikenne ta jihar ogun.

Kungiyar ASUU Ta Koka Kan Kara Kudin Makaranta

malamin mai suna Kolawole Shonuga ya kwace takardun daya daga cikin daliban bayan ya kama shi yana satar amsa a lokacin da yake tsaron ’yan aji hudu (SS1) da ke zana jarrabawar zangon karshe na bana.

Advertisement

Sai dai bayan an tashi daga makarantar ne dalibin mai suna Ashimi Adebanjo ya hado kan abokansa inda suka yi kungiya suka dirar wa malamin a kofar makaranta kuma suka lakada masa duka.

Bayanai sun ce tuni lamarin ya shiga hannun hukuma, inda jami’an ’yan sanda suka cafke akalla dalibai 10 da ake zargi kamar yadda kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Omotola Odutola ya sanar.

Advertisement

Shugaban Kungiyar Jami’an Makarantun Sakandire na jihar, Felix Agbesanwa, ya bayyana fushinsa kan lamarin da cewa dole ne daliban su girbi abin da suka shuka.

Irin haka dai ta faru kusan sau hudu a watan Oktoban 2021, inda aka samu dalibai sun ci zarafin malamansu a makarantun Gwamnatin Jihar Ogun.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending