Connect with us

News

Trump Zai Rushe Wasu Hukumomi, Ciki Har Da VOA

Published

on

71867225 803

 

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya rattaba hannu kan sabuwar doka da za ta takaita ayyukan wasu hukumomi guda shida tare da rushe wasu gaba daya, ciki har da kafar yada labarai ta Voice of America (VOA).

Advertisement

Hukumomin da abin ya shafa sun hada da gidajen adana kayan tarihi, dakunan karatu, da bangaren kula da marasa galihu. A cewar Trump, wadannan hukumomi na yada bayanai da ke nuna masa kyara.

Kwamitin Tabbatar Da Tsaro A Kano Ya Kaddamar Da Gagarumin Samame Kan ‘Yan Daba Da Masu Shaye-shaye

Sabuwar daraktar da za ta jagoranci wannan rushewa ita ce ‘yar jarida Kari Lake, wadda aka nada domin aiwatar da sabon tsarin. VOA, wacce aka kafa shekaru 80 da suka wuce, na yada shirye-shiryenta a harsuna 40 ta rediyo, talabijin, da intanet.

Advertisement

Matakin ya jawo cece-kuce, inda masu sukar sa ke ganin hakan a matsayin yunkuri na dakile ‘yancin yada labarai a Amurka.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending