News
Manyan ‘Yan Adawar Najeriya Sun Bukaci Majalisa Ta Yi Watsi da Bukatar Shugaba Tinubu Kan Rivers
Manyan ‘yan adawar Najeriya sun roƙi Majalisar Dokokin ƙasar da ta yi watsi da bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na kafa dokar ta-baci a Jihar Rivers tare da dakatar da gwamna da ‘yan majalisar dokokin jihar.
Yayin wata ganawa ta musamman da manema labarai, wacce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya jagoranta, ‘yan adawar sun zargi Shugaba Tinubu da wuce gona da iri da kuma neman durkusar da dimokiradiyya a Najeriya.
Gwamnatin Kebbi Ta Musanta Rufe Jami’ar Aliero Saboda Cutar Sankarau
Atiku ya yi nuni da cewa matakin da Shugaba Tinubu ke shirin ɗauka ya ci karo da kundin dokokin ƙasa da hukuncin Kotun Koli. Saboda haka, ya bukaci Majalisar Dokoki da ta yi abinda ya dace wajen ƙin amincewa da bukatar dakatar da Gwamnan Rivers da ‘yan majalisar dokokin jihar.
Hakazalika, Atiku ya bukaci bangaren shari’a da ya tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ‘yancinsa na kashin kansa, tare da bayyana matakin Tinubu a matsayin haramcacce.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, da kuma Inusa Tanko na jam’iyyar Labour. Sai dai wasu jiga-jigan adawa kamar tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, da tsohon shugaban jam’iyyar APC sun nemi gafarar rashin halarta saboda wasu uzuri.
