Connect with us

News

NYSC Ta Sanar Da Sabuwar Ranar Fara Biyan Alawus N77,000

Published

on

FB IMG 1742486739996

 

Darakta Janar na Hukumar Matasa Masu Yi wa Ƙasa Hidima (NYSC), Brigediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, ya tabbatar da cewa matasa masu hidimtawa ƙasa za su fara karɓar sabon alawus na N77,000 daga ƙarshen watan Maris.

Advertisement

Ana sa ran gwamnatin tarayya za ta kashe Naira biliyan 430.7 wajen aiwatar da sabon tsarin biyan alawus ɗin, wanda aka haɓaka daga N33,000 zuwa N77,000.

Zargin Cin Hanci: ‘Yan Majalisa Sun Karbi Dala 25,000 Kowane Don Goyon Bayan Dokar Ta-Baci

Tun bayan amincewar gwamnatin tarayya da ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata, an dade ana dakon fara biyan sabon alawus ɗin ga matasan NYSC.

Advertisement

A baya-bayan nan, wata ‘yar hidimar ƙasa a Jihar Lagos, Ushei Uguamaye, ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda tsadar kayan masarufi ke wahalar da su, tana mai cewa tsohon alawus ɗin N33,000 bai wadatar da su ba.

Sabon alawus ɗin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta ƙorafi kan hauhawar farashin kayayyakia ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending