Connect with us

News

Mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina Ta Rasu Tana Da Shekaru 93

Published

on

IMG 20250323 WA0007 1

 

Hajiya Safara’u Umaru Barebari, mahaifiyar Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ta riga mu gidan gaskiya tana da shekaru 93.

Advertisement

Sanarwar rasuwarta ta fito ne daga Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, wanda ya bayyana cewa:

Ramadan Na Kara Nisa: Hankula Sun Karkata Daga Siyan Abincin Buda Baki Zuwa Shirye-shiryen Sallah

“Ciki da alhini, Gwamnatin Jihar Katsina na sanar da rasuwar Hajiya Safara’u Umaru Barebari, mahaifiyar Gwamna Dikko Umaru Radda.”

Advertisement

Hajiya Safara’u ta rasu a daren jiya, tana da shekaru 93 a duniya. Ta kasance mace mai jajircewa da basira, wacce ta rayu cikin daraja da mutunci.

Ta bar ‘ya’ya da jikoki da tattaba-kai da dama, ciki har da Hakimin Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, da Hajiya Hauwa Umar Radda, tsohuwar matar marigayi Shugaban Kasa, Umaru Musa Yar’adua.

Advertisement

Allah Ya jikanta da rahama, Ya gafarta mata kurakuranta, Ya kuma ba iyalanta hakurin jure wannan rashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending