News
Ruɗani Ya Karu Yayin Da Bayero Da Sanusi II Ke Shirin Hawan Sallah A Kano
Al’ummar Jihar Kano sun shiga ruɗani yayin da rikicin masarautar jihar ya ɗauki sabon salo, biyo bayan shirye-shiryen hawan sallah na sarakunan biyu, Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II
Duk da shari’ar da ke gudana kan rikicin masarautar, bangarorin biyu sun nuna aniyarsu ta gudanar da hawan salla, lamarin da ke ƙara haifar da ce-ce-ku-ce da fargabar tashin hankali a jihar.
Wata wasiƙa da Sakataren Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, ta bayyana shirinsa na gudanar da Hawan Daushe da Hawan Nassarawa. Wannan na zuwa ne bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, da ya fara shirye-shiryen hawan salla.
Jami’an Hukumar NDLEA Sun Cafke ‘Yar Indiya Da Hodar Iblis Kilogiram 11 A Filin Jirgin Kano
Tun bayan sauke Sanusi II daga sarauta a 2020 da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero, rikicin masarautar Kano bai gushe ba. A shekarar 2024, Majalisar Dokokin Kano ta rushe masarautun da tsohon gwamna Ganduje ya kirkira tare da mayar da Sanusi II a matsayin sarki, matakin da ya kai ga rikici na shari’a.
A halin yanzu, yayin da gwamanti da hukumomin tsaro ba su bayyana matsayinsu kan rikicin ba, jama’a na nuna damuwa kan yiwuwar barkewar rikici idan duka sarakunan suka ci gaba da shirye-shiryensu.
Dattijon Kano, Malam Haladu Bello, ya ce: “Na sha ganin hawan salla mai armashi da kuma wanda ke da matsaloli, amma wannan yana da ban tsoro.”kamar yanda Jaridar AMINIYA ta ruwaito
Yayin da bikin salla ke ƙaratowa, idanu na kan matakan da hukumomi za su ɗauka domin kaucewa rikicin da ka iya tasowa daga wannan rikici mai ci
ke da ruɗani.
