Connect with us

News

Gobara Ta Tashi a Gidan Mai A Neja Bayan Fashewar Tanka

Published

on

niger

Wata gobara mai muni ta tashi a gidan mai na A.A. Rano da ke Kontagora, Jihar Neja, bayan da wata tanka ɗauke da man fetur ta kama da wuta yayin sauke mai.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na daren Lahadi, kusa da Asibitin Gaba, inda aka ce gobarar ta fara ne sakamakon fashewar tankar. Shaidu sun bayyana cewa wutar ta bazu cikin sauri, lamarin da ya jefa jama’a cikin tsoro, kasancewar sauran tankunan da ke wurin cike suke da fetur.

Advertisement

Bututun Iskar Gas Ya Sake Fashewa A Ribas: Wata Gobara Mai Ƙarfi Ta Tashi

Jami’an kashe gobara sun garzaya wajen domin shawo kan lamarin, amma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, wutar na ci gaba da yaɗuwa.

Wani shaidan gani da ido, Abba Mohammed, ya ce babu wanda aka ruwaito ya rasa ransa, amma jama’a sun ruga don tsira da rayukansu.

Advertisement

Ƙoƙarin jin ta bakin Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ya ci tura,

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending