News
Bashin Najeriya Ya Kai Naira Tiriliyan N144.67 A 2024 – Rahoton DMO
Ofishin Kula da Basussuka na Najeriya (DMO) ya bayyana cewa bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan N144.67 ($94.23 biliyan) a ranar 31 ga Disamba, 2024, wanda ya nuna karuwar kashi 48.58 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan N97.34 da aka ruwaito a Disamba 2023.
Rahoton ya nuna cewa, bashin ya karu da Naira tiriliyan N2.35, ko kashi 1.65 cikin 100, daga Naira tiriliyan N142.32 da aka ruwaito a karshen Satumba 2024 zuwa Naira tiriliyan N144.67 a Disamba 2024.
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Tsawaita NYSC Zuwa Shekaru Biyu – Ministan Ilimi
Bincike ya nuna cewa bashin kasashen waje ya karu da kashi 83.89 cikin 100, daga Naira tiriliyan N38.22 ($42.50 biliyan) a Disamba 2023 zuwa Naira tiriliyan N70.29 ($45.78 biliyan) a Disamba 2024. Wannan karuwar ta samo asali ne daga sabon bashin da aka karɓa daga ƙasashen waje da kuma raguwar darajar Naira.
A gefe guda, bashin cikin gida ya kai Naira tiriliyan N74.38 ($48.44 biliyan) a Disamba 2024, wanda ya nuna ƙaruwa daga Naira tiriliyan N73.43 ($45.87 biliyan) da aka ruwaito a Satumba 2024. Gwamnatin tarayya ce ta fi karɓar wannan bashin, inda bashin ya karu daga Naira tiriliyan N69.22 a Yuni zuwa Naira tiriliyan N70.41 a Disamba.
A cikin watan Disamba na 2024, gwamnatin tarayya ta tara dala biliyan $2.2 ta hanyar sayar da takardun bashi na Eurobond, wanda ya nuna komawarta kasuwannin hada-hadar kudi na duniya. Wannan kudade ana sa ran za su taimaka wajen tallafawa kasafin kudin 2024, musamman ma ganin yadda ake fuskantar karancin kudaden shiga da kuma hauhawar kashe kudi.
