Connect with us

News

2025: Za Mu Yi Aikin Hajji Da Ba A Taba Yin Irinsa Ba A Nijeriya – Sheikh Abdullahi Sale Usman

Published

on

IMG 20250416 WA0021

DAGA ISMAIL YUSUF MAKWARARI

Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nijeriya, Sheikh Abdullahi Sale Usman, ya bayyana cewa hukumar na shirin gudanar da aikin Hajji mafi inganci da tarihi ba zai manta da shi ba a shekarar 2025. Ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa ta musamman da aka yi da shi kai tsaye a gidan talabijin na AFRICA TV3 da ke Kano, karkashin jagorancin Babban Daraktan tashar, Dr. Tijjani.

Advertisement

A cewar Sheikh Abdullahi, babban burinsa shi ne ganin Alhazan Nijeriya sun gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali, lafiya da jin daɗi, ba tare da fuskantar wata matsala ba. Ya ce hukumar za ta yi amfani da kwarewarta da gogewar da ta samu a baya wajen tabbatar da wannan buri.

Hukumar Tace Fina-finai Ta Kano Ta Fara Kamen Baburan Adai-daita Sahu Masu Hotuna Da Rubuce-Rubucen Batsa

“Ina fatan aikin Hajjin bana zai kasance mafi nagarta da tarihi bai taba gani ba. Mun tanadi masauki ga maniyyata kimanin 52,000 daga jihohi daban-daban, tare da ware masauki na musamman ga maniyyatan da ke bin jiragen yawon shakatawa (Tour Operators) har 20,000,” in ji shi.

Advertisement

Sheikh Abdullahi ya jaddada cewa hukumar ta mayar da hankali musamman kan batutuwan da suka shafi masauki, abinci, da zaman Mina – inda ake fuskantar ƙalubale mafi yawa. Ya ce an ɗauki matakan da suka dace wajen tabbatar da cewa alhazan za su samu jin daɗin zaman su a wuraren ibada.

“Mun yi aiki kafada da kafada da masu kula da masaukanmu a Mina da Arfa don samar da ban dakuna masu yawa da sauran kayayyakin more rayuwa,” in ji shi.

Advertisement

Ragin Kuɗin Kujerar Hajji

Sheikh Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar ta cimma nasarar rage farashin aikin Hajji na bana da naira biliyan 54, duk da tashin da darajar Dala ta yi. Wannan ya rage nauyi a kan alhazai, kuma ya ce hakan ba zai yiwu ba sai da taimakon Allah da goyon bayan gwamnati.

Advertisement

Kulawa Da Lafiyar Alhazai

Game da lafiyar alhazai, Sheikh Abdullahi ya bayyana cewa an tanadi dukkan abin da ake bukata: daga likitoci ƙwararru, zuwa magunguna da motoci masu ɗaukar marasa lafiya. Ya kuma nuna godiya ga Ministan Lafiya bisa tallafin da yake bayarwa.

Advertisement

“Za mu cigaba da wayar da kan alhazai kan rahotannin da ke nuna cewa bana ana sa ran samun tsananin zafin rana. Don haka muna ba da shawarwari bisa ga abin da masana suka bayar.”

Martani Ga Caccakar Da Ba Ta Da Tushe

Advertisement

Shugaban hukumar ya yi kira ga masu yada jita-jita da suka dakata da watsa labaran ƙarya game da hukumar. Ya bukaci masu amfani da kafafen sadarwa da su rika tuntubar hukumar kafin yada wani rahoto, don tabbatar da sahihancin sa.

Sheikh Abdullahi ya godewa shugaba Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, bisa gudunmowar da suka bayar wajen ganin an samu nasarar wannan aiki mai tsarki. Haka kuma ya yaba da hadin kai daga hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

Advertisement

“Manufata ita ce ganin cewa alhazai sun gudanar da Hajji cikin walwala da farin ciki. Wannan shi ne burina kuma ina da yakinin za mu cimma hakan, in sha Allah.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending