News
ASUU Ta Ce Za Ta Maka JAMB Kotu Kan Mummunan Sakamakon UTME
Kungiyar Malaman Jami’a ta Kasa (ASUU), reshen Jami’ar Nsukka (UNN), ta bayyana cewa za ta dauki matakin shari’a a kan Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandare ta Kasa (JAMB), saboda yadda dalibai da dama – musamman na Kudu Maso Gabas – suka fadi jarabawar UTME ta bana.
Shugaban ASUU na UNN, Kwamared Oyibo Eze, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a garin Nsukka da ke Jihar Enugu a ranar Laraba.
Kwamared Eze ya ce, “Shiyyar da ta fi fuskantar faduwa a jarabawar UTME ita ce Kudu Maso Gabas. Wannan wani nau’i ne na gangan da JAMB ke yi domin hana yaran wannan yanki damar shiga jami’o’in kasar nan.”
Ya ce ASUU za ta kalubalanci sakamakon a kotu idan har JAMB ta gaza sake duba lamarin da kuma ba daliban da suka cancanta makin da ya dace.
“Ofishina ya cika da koke-koken iyaye da dalibai kan yadda aka danne su a wannan sakamako. Ba za mu yi shiru ba,” in ji shi.
Kwamared Oyibo ya kuma bukaci gwamnonin jihohin Kudu Maso Gabas da su tashi tsaye domin kare ‘ya’yan jiharsu, yana mai cewa ya kamata a dauki matakin gaggawa domin dakile abin da ya kira rashin adalci da wariya a fagen ilimi.
A gefe guda kuwa, shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewa hukumar na shirin sake gudanar da jarabawa ga wasu daliban da ke jihohin Kudu Maso Gabas da kuma Legas.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News4 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News6 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
