Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Raba Kujerun Karatu Ga Makarantu 200 A Karamar Hukumar Rogo

Published

on

Abba

Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na farfado da harkar ilimi, ta hanyar raba kujerun karatu ga makarantun da ke fadin jihar.

A karkashin wannan shiri, a ranar Asabar, karamar hukumar Rogo ta kaddamar da rabon kujerun aji ga daliban makarantu 200 da ke cikin yankin.

Advertisement

Kamfanin NNPCL Ya Rufe Matatar Mai Ta Fatakwal

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a harabar sakatariyar karamar hukumar, inda Kwamishinan Ilimi na karamar hukumar, Malam Muhammad Abdullahi Bari, ya wakilci Shugaban Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Abubakar Mustapha Rogo.

Malam Bari ya bayyana cewa wannan mataki wani bangare ne na shirin gwamnatin Kano na tabbatar da ingantaccen yanayin koyarwa da koyo, musamman a makarantun gwamnati.

Advertisement

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a, Karamar Hukumar Rogo Abdu Bako Abdullahi ta turawa da Jaridar INDA RANKA

Sanarwar ta bukaci shugabannin makarantun da suka karbi kujerun da su tabbatar da amfani da su yadda ya kamata, tare da kula da su domin dorewar amfani.

Advertisement

A nasa jawabin, Sakatare na Ilimi na karamar hukumar Rogo, Malam Sule Imam, ya bayyana cewa shirye-shiryen gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na farfado da ilimi sun fara haifar da gagarumin sakamako.

Ya ce rabon kujerun zai gudana ne cikin adalci da gaskiya, tare da tabbatar da cewa duk wata makaranta da ke bukata za ta samu nata rabo.

Advertisement

Ya kuma tabbatar da goyon bayan hukumar ilimi ta karamar hukumar ga dukkan manufofin gwamnatin jihar da suka shafi ci gaban ilimi da inganta rayuwar al’umma.

Wannan shiri na daga cikin jajircewar gwamnatin jihar wajen inganta ilimi da samar da kyakkyawan yanayin karatu ga yara ’yan asalin jihar Kano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending