News
JAMB: Hukuma Ta Kama Mutum 20 Bisa Zargin Kutse A Sakamakon Jarabawar UTME Ta 2025
Hukumar ’Yan Sanda tare da haɗin guiwar jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) sun kama mutum 20 da ake zargi da kutse cikin tsarin sakamakon jarabawar UTME ta shekarar 2025 da Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ke gudanarwa.
Rahotannin da aka samu daga kafafen watsa labarai sun bayyana cewa, ana zargin waɗanda aka kama da kasancewa mambobi ne a wata babbar ƙungiyar masu kutse da ake kyautata zaton tana da sama da mutum 100 a faɗin ƙasar nan.
Gwamnatin Kano Ta Raba Kujerun Karatu Ga Makarantu 200 A Karamar Hukumar Rogo
Binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar ta girka wasu na’urori na musamman a cikin kwamfutocin da ake amfani da su a cibiyoyin gudanar da jarabawa na CBT, wanda hakan ya ba su damar shiga shafin JAMB daga nesa ba tare da izini ba.
Wata majiya mai tushe da ke da masaniya kan lamarin ta bayyana cewa burin ƙungiyar shi ne rage sahihancin tsarin jarabawar CBT, tare da ƙoƙarin hana ci gaba da amfani da tsarin a sauran jarabawowin ƙasa kamar NECO da WAEC.
Sai dai zuwa yanzu, Hukumar JAMB ba ta fitar da wata sanarwa kai tsaye kan wannan batu ba. Sai dai rahotanni sun nuna cewa hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakkun bayanai da kuma tantance ko akwai sauran mutane da ke da hannu a cikin wannan aiki na kutse.
