News
JAMB Ta Saki Sakamakon Ɗaliban Da Suka Sake Rubuta Jarrabawa
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta fitar da sakamakon ɗaliban da suka sake rubuta jarabawar UTME ta bana.
JAMB ta ce an sake jarrabawar ce saboda tsaikon da ya faru lokacin da aka fara jarrabawar a watan da ya gabata, musamman a wasu cibiyoyi a Legas da jihohin Kudu maso Gabas.
JAMB: Hukuma Ta Kama Mutum 20 Bisa Zargin Kutse A Sakamakon Jarabawar UTME Ta 2025
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar ranar Lahadi, ya ce ɗalibai 336,845 ne aka sake ba damar rubuta jarrabawar, amma daga cikinsu, 21,082 ba su halarta ba.
Ya kuma ce hukumar ta gano wasu ayyukan satar jarrabawa da ɗalibai da wasu cibiyoyin jarrabawa ke aikatawa, kuma tuni an fara daukar mataki a kai.
JAMB ta ce ta sake shirya jarrabawar ne domin tabbatar da adalci ga ɗaliban da suka fuskanci matsala, da kuma tabbatar da cewa kowa ya samu damar daidai wajen nuna abin da ya koya.
-
News7 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News3 days agoKotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano
-
News5 days agoƘalubalen Da Masu Ƙananan Sana’o’i Ke Fuskanta Saboda Ƙarancin Wutar Lantarki A Kano
