News
Matar Aure Ta Aikata Kisan Kishiyarta A Gaban Mijinta A Katsina
Rundunar ’yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kama wata matar aure mai suna Rabi’atu Labaran, mai shekara 23, bisa zargin daba wa kishiyarta wuka har ta yi ajalinta a Sabon Garin Daura, karamar hukumar Daura ta jihar Katsina.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Dadi da ke bayan makarantar firamare, inda mijin matan, Nasiru Yusuf, ya dawo daga kasuwa ya tarar da uwargidansa, Zainab, kwance cikin jini, lamarin da ya tilasta masa garzaya da ita zuwa Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke garin Daura.
NUJ Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Tallafawa Manoma Kafin Damina
Sai dai kafin a isa asibitin, likitoci sun tabbatar da rasuwarta.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya shaida wa manema labarai cewa binciken farko ya nuna akwai saɓani tsakanin matan biyu, wanda daga bisani ya rikide zuwa rikici mai tsanani.
A cewarsa, Rabi’atu ta amsa cewa ita ce ta daba wa kishiyar ta wuka, kuma hakan ya janyo mutuwarta.
Ya ce tuni aka fara gudanar da cikakken bincike a kan lamarin, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da wadda ake zargi a gaban kotu domin girbar abin da ta shuka.
DSP Abubakar ya ƙara da cewa rundunar ’yan sanda ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da an hukunta masu aikata laifuka musamman masu nasaba da kisan kai da kuma rikice-rikicen cikin gida.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, CP Bello Shehu, ya bukaci ma’aurata da su rika zama lafiya da juna tare da guje wa duk wata matsala da ka iya rikidewa zuwa tashin hankali.
Ya ce rikice-rikicen cikin gida kan haifar da babbar illa ga zaman lafiya da ci gaban iyali, inda ya jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyin jama’a.
