News
Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Wike Kan Kwace Filaye 4,794 a Abuja, Ya Ba da Wa’adi
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shirin kwace filaye 4,794 da gwamnatin tarayya ta soma karɓa a Abuja saboda rashin biyan haya na ƙasa na tsawon shekaru.
A ranar Litinin da ta gabata ne Ma’aikatar Kula da Filaye ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta fara kulle gine-gine da dama da ta ce ba su biya bashin kuɗin haya ba.
RUWAN SHA YA ZAMA BARAZANA: Ƙauyukan Da Mutane, Jakuna Da Karnuka Ke Shan Ruwa Waje Ɗaya A Kano
Daraktan kula da harkokin filaye na FCT, Chijioke Nwankwoeze, ya ce gwamnati ta yanke shawarar ba masu filayen wata sabuwar dama ta makonni biyu domin su biya bashin da ake bin su, ko kuma su fuskanci rasa kadarorinsu gaba ɗaya.
Filayen da abin ya shafa sun haɗa da na hukumomin gwamnati, kamfanoni da na ‘yan kasuwa masu zaman kansu a manyan unguwannin Abuja kamar Maitama, Asokoro, Wuse, Garki da Guzape.
A karkashin sabon tsarin da aka fito da shi, an ware farashi daban-daban ga yankuna:
Masu filaye a Central Area za su biya Naira miliyan biyar
Maitama, Asokoro, Wuse II da Guzape – Naira miliyan uku
Garki I, Garki II da Wuse I – Naira miliyan biyu
Haka kuma, gwamnati ta umarci duk wanda ya sayi fili daga wani amma bai samu amincewar Minista ba, ko kuma bai yi rijistar takardun mallaka ba, da ya kammala hakan cikin kwanaki 14.
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce ba za a cigaba da lamunci da masu kauce wa biyan hakkokin da suka rataya a kansu ba. Ya bukaci masu kadarori da su biya hakkokin su domin a samu ci gaba da tsaftar birnin Abuja.
