News
AMBALIYAR RUWA: Mutum 21 Sun Rasa Rayukansu, Gidaje 50 Sun Lalace A Neja
Akalla mutane 21 ne suka mutu, yayin da wasu goma (10) har yanzu ba a gano su ba, sakamakon mummunar ambaliya da ta shafi unguwannin Tiffin Maza da Anguwan Hausawa a karamar hukumar Mokwa ta Jihar Neja.
Ambaliyar, wadda ta faru bayan ruwan sama mai ƙarfi da aka yi a daren Laraba, ta lalata gidaje fiye da hamsin (50) tare da yanke hanyoyin mota da ke da muhimmanci ga mu’amala da harkokin yau da kullum a yankin.
Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Malam Abdullahi Baba Arah, ya bayyana cewa hukumar ta samu rahoton afkuwar “mummunar ambaliya” da ta yi sanadin mutuwar mutane da kuma bacewar wasu.
A cewarsa, daga cikin mutane 33 da ruwa ya dauke, an samu nasarar ceto uku da ransu, yayin da ake ci gaba da bincike da aikin ceto domin gano wadanda suka bace.
Ya ce an fara daukar matakan gaggawa domin tallafa wa iyalan da bala’in ya rutsa da su, tare da yin hadin gwiwa da hukumomin tsaro da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.
Rahotanni sun nuna cewa wannan ambaliya na daga cikin mafi muni da aka fuskanta a Mokwa cikin ‘yan shekarun nan, lamarin da ke sake bayyana bukatar ingantattun hanyoyin kare muhalli da rage illar sauyin yanayi.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
