News
NUJ Ta Karrama Gwamna Abba Kabir Yusuf A Bikin Cika Shekaru 70

Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta kasa (NUJ) ta karrama Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da lambar yabo ta musamman bisa goyon bayan da yake bai wa aikin jaridu.
An bayar da lambar karramawar ne a wani biki da NUJ ta shirya domin cika shekaru 70 da kafuwarta a birnin Abuja, inda mataimakin gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karɓa a madadin gwamnan.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Alhaji Muhammad Idris, ne ya miƙa lambar girmamawar.
Shugaban NUJ na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya ce an zaɓi Gwamna Abba ne saboda irin goyon bayan da yake bai wa kafafen yaɗa labarai da kuma jajircewarsa wajen cigaban ƙasa, kare ’yancin fadar albarkacin baki da inganta shugabanci na gari.
A nasa jawabin, mataimakin gwamnan ya taya Gwamna Abba murna, yana mai cewa karramawar ta nuna yadda gwamnatin Kano ke mutunta aikin jarida da ma dimokuraɗiyya baki ɗaya.
Kwamared Gwarzo ya kuma bayyana cewa Jihar Kano za ta karɓi bakuncin taron Kungiyar NUJ na gaba.
-
News5 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News2 days ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News5 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
