News
Yadda Cutar Amai da Gudawa Ta Kama Dalibai 81 A Makarantar Gwamnati A Kaduna
Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kaduna ta tabbatar da barkewar cutar amai da gudawa a Makarantar Sakandare ta Gwamnati ta ’Yan Mata (GGSS & GJSS), da ke Kawo, inda dalibai 81 suka kamu da cutar, ciki har da wasu 15 da aka kwantar da su a asibiti.
A cewar sanarwar da ma’aikatar ta fitar ranar Juma’a, cutar ta fi shafar daliban da ke tsakanin shekaru 16 zuwa 17.
Wasu Matasa Sun Damke Masu Kwacen Waya, Sun Mika Su Hannun ’Yan Sandan A Kano
Kwamitin bincike na gaggawa karkashin jagorancin Dakta Jeremiah Diako, Likitan Nazarin Cututtuka na jihar, ya bayyana cewa an dauki matakin gaggawa wajen kai wadanda cutar ta fi shafa zuwa Asibitin Gwamnati na Kawo domin kulawa ta musamman.
“Dukkanin wadanda aka kwantar sun samu sauki kuma an sallame su,” in ji Diako.
Ma’aikatar ta ce ta dauki wasu matakai domin hana barkewar cutar a nan gaba, ciki har da:
Gina tsarin bayar da rahoton cututtuka cikin gaggawa daga makarantu,
Samar da tsarin sa ido kai tsaye a kan tsaftar abinci da ruwan sha,
Koyar da ma’aikatan makarantu yadda za su kula da tsafta da kiwon lafiya,
Da kuma karfafa tsarin rigakafi da daukar matakin gaggawa a makarantu da unguwanni.
Ma’aikatar Lafiyar ta Jihar Kaduna ta jaddada cewa akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin hukumomi da iyaye wajen tabbatar da tsafta da kula da lafiyar dalibai.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya bayyana cewa barkewar cutar amai da gudawa a makarantu ba sabon abu ba ne, inda lamarin ke kara jaddada bukatar daukar matakai na musamman da dindindin don kare rayuwar yara.
