News
NLC Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta yi barazanar shiga yajin aiki na ƙasa sakamakon tsanantar rayuwa da kuma ƙarin tabarbarewar tsaro da ke addabar ’yan Najeriya.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wani taron kwamitin zartaswa da ta gudanar a birnin Abeokuta, Jihar Ogun, inda ta nuna damuwa matuƙa kan yadda tattalin arzikin ƙasa ke cigaba da durƙushewa, yayin da dimokuraɗiyya ke fuskantar ƙalubale.
A cewar ƙungiyar, ma’aikata da al’umma masu ƙaramin karfi na shan wuya a ƙarkashin hauhawar farashin kayayyaki da hauhawar haraji, lamarin da ke ci gaba da rage musu ƙarfin siye da kuma jefa su cikin matsin rayuwa.
> “Ba za mu ci gaba da zama shiru ba a yayin da gwamnati ke nuna halin ko-in-kula game da wahalhalun da ma’aikata da talakawa ke ciki,” in ji sanarwar da NLC ta fitar bayan taron.
NLC ta ce idan gwamnati ta gaza ɗaukar matakin gaggawa don rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa da kuma kawo ƙarshen matsalar tsaro, babu sauran mafita illa ɗaukar matakin yajin aiki domin kare rayuwar ’yan ƙasa.
Ƙungiyar ta kuma buƙaci shugabannin siyasa su daina yin kallo ne kawai ba tare da tsayawa tsayin daka don kawo sauyi ba, domin a cewarta, halin da ake ciki na iya kai wa ga rikicewar zamantakewa da durƙushewar ƙasa gaba ɗaya.
“Dole ne gwamnati ta fahimci cewa jinkiri wajen ɗaukar mataki yana nufin ƙara dagula al’amura, kuma mu a matsayimmu na wakilan ’yan ƙasa, za mu tashi tsaye don kare martabar rayuwarmu,” in ji ƙungiyar.
A halin da ake ciki, NLC ta ce tana ci gaba da tuntubar sauran ƙungiyoyin ƙwadago da ƙungiyoyin farar hula domin ɗaukar matakin da ya dace nan gaba kadan.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
