Connect with us

News

An Ciro Maciji Nau’in Kububuwa Daga Takalmin Mai Gadi

Published

on

122433449

Wani mai gadi da ke aiki a wani kamfani a yankin Mhape MIDC da ke birnin Navi Mumbai dake ƙasar Indiya, ya shiga cikin firgici a safiyar Litinin bayan ya gano wani babban maciji nau’in kububuwa a cikin ɗaya daga cikin takalmansa.

Jaridar THE TIMES OF INDIA ta ruwaito cewa mai gadin ya ajiye takalmansa ne a wajen ɗakin tsaro saboda ruwan sama da aka yi a daren jiya. Da safe, lokacin da zai sa takalman, sai ya lura da wani motsi a ciki. Lokacin da ya leka don duba abin da ke ciki, sai ya tarar da wani babban maciji yana nannade yana barci a cikin takalmin.

Advertisement

‎Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa Ya Sauya Sheƙa Zuwa ADC

Daga nan ne aka sanar da wani ƙwararren mai kama macizai mai suna Akshay Dange, wanda ya iso cikin hanzari, ya kuma ciro macijin cikin kwarewa ba tare da wata matsala ba. Daga bisani, an mayar da macijin cikin daji domin ci gaba da rayuwarsa a halittarsa ta dabi’a.

Masana sun ce a irin wannan lokaci na damina, ana yawan fuskantar faruwar irin wannan lamari, inda macizai ke shigewa cikin takalma, jakunkuna, huluna da wasu wurare da suka bushe domin neman mafaka daga sanyi da ruwa.

Advertisement

Sun kuma shawarci jama’a da su rika duba kayansu da kyau, musamman a lokacin damina, domin kauce wa haɗurran da za su iya zama barazana ga lafiyar rayuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending