Connect with us

Politics

Aishatu Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

Published

on

download (2)

Tsohuwar ‘yar takarar gwamnan Jihar Adamawa a jam’iyyar APC, Sanata Aishatu Dahiru Binani, ta sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC.

Rahotanni sun bayyana cewa Binani ta yanke shawarar barin APC ne saboda rikicin cikin gida da kuma yadda jam’iyyar ke gudanar da lamuranta a jihar Adamawa da kasa baki ɗaya, musamman bayan gazawar da ta fuskanta a zaɓen 2023.

Advertisement

An Kama Wani Tsohon Fursuna Da Zargin Damfarar Mata 17 A Kano

An bayyana cewa ta gana da manyan shugabannin jam’iyyar ADC kafin yanke shawarar shiga cikinta, inda suka tabbatar mata da cikakken goyon baya.

Tun kafin yanzu, Binani ta kasance daya daga cikin fitattun mata a siyasar Najeriya, kuma ta kafa tarihi a 2023. Masu fashin baki na ganin shigarta ADC na iya ƙarfafa jam’iyyar a yankin Arewa maso Gabas da ma kasa baki ɗaya, musamman idan ta bayyana sha’awarta ta sake tsayawa takara a 2027.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending