Connect with us

News

Jami’an Hukumar NAFDAC Sun lalata Tramadol Guda 491,000 A Kano ‎

Published

on

Tramadol 750x430

Jami’an Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, wato NAFDAC, sun lalata Tramadol guda 491,000 da aka kama a Jihar Kano, a wani yunkuri na kare lafiyar jama’a daga barazanar haramtattun magunguna.

‎Tramadol ɗin na nau’in 225mg an kama su ne a ranar 28 ga watan Mayu, 2025, lokacin da jami’an Hukumar Kwastam reshen Kano da Jigawa suka cafke su a yankin Mai Gatari da ke kan iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Advertisement

Jihar Nasarawa Ba Mafaka Bace Ga Masu Laifi — Inji Gwamna Sule

‎An bayyana cewa waɗanda suka shigo da magungunan sun gudu bayan jami’an kwastam sun dakile yunkurin su.

‎Babban daraktan bincike da aiwatar da dokoki na NAFDAC, Dr. Martins Iluyomade, ne ya jagoranci kona kwayoyin a madadin shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.

Advertisement

‎Farfesa Adeyeye ta ce, “Adadin Tramadol da aka kama ya kai 491 jarka, wato kimanin 491,000 a dunkule. An ƙiyasta darajar su a kasuwa da naira miliyan 91.”

 

Advertisement

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending