Connect with us

News

Cutar Amai da Gudawa Ta Yi Ajalin Mutum 12, Ta Kwantar da Fiye Da 230 A Asibiti A Neja

Published

on

Gwamnatin Jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutane 12 tare da kwantar da wasu 230 a asibitoci, sakamakon barkewar cutar amai da gudawa da ta bulla a wasu kananan hukumomi shida a jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa cutar ta fara bayyana ne a ranar Lahadi da ta gabata a Karamar Hukumar Shiroro, kafin daga bisani ta yadu zuwa Minna, Bosso, Magama, Rafi da Munya.

Advertisement

Yanzu APC ta fara numfasawa a Kano

Kwamishinan Lafiya na Matakin Farko a jihar, Dakta Ibrahim Dangana, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta dauki matakan gaggawa na dakile yaduwar cutar, inda ta kafa cibiyoyin killace masu dauke da ita a yankunan da lamarin ya fi kamari.

A cewarsa, “A halin yanzu, muna da mutane 239 da suka kamu da cutar, kuma suna karbar kulawa a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da muka tanada. Haka kuma mun bude wata cibiya ta musamman a tsohon Asibitin Sanata Idris Kuta da ke Minna domin killace masu cutar.”

Advertisement

Dakta Dangana ya ce gwamnati ta tura kwararrun jami’an lafiya zuwa wuraren da cutar ta bulla domin taimakawa wajen ba da kulawa gaggawa da kuma dakile yaduwar cutar.

Ya kuma bukaci al’umma da su kara himma wajen kiyaye tsaftar muhalli, tsaftar abinci da kuma gujewa shan ruwa ko amfani da ababen amfani da ba su da tsafta.

Advertisement

 

 

Advertisement

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending